Tsallake zuwa abun ciki

circa 605–538 BC

The Babylonian Exile

Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.

1,784 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Daniyel 8:25kusan 553 K.H.

    Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.

  2. Daniyel 8:26kusan 553 K.H.

    “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.”

  3. Daniyel 8:27kusan 553 K.H.

    Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata.

  4. Daniyel 9:1kusan 538 K.H.

    A shekara ta fari da mulkin Dariyus ɗan Zerzes (wanda yake Bamediye), wanda aka mai da shi sarki a masarautar Babiloniyawa

  5. Daniyel 9:2kusan 538 K.H.

    a shekara ta farko ta mulkinsa, ni, Daniyel na gane daga cikin littattafai, bisa ga maganar Ubangiji da aka faɗa wa annabi Irmiya, cewa zaman Urushalima kango zai kai shekara saba’in.

  6. Daniyel 9:3kusan 538 K.H.

    Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  7. Daniyel 9:4kusan 538 K.H.

    Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,

  8. Daniyel 9:5kusan 538 K.H.

    mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.

  9. Daniyel 9:6kusan 538 K.H.

    Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.

  10. Daniyel 9:7kusan 538 K.H.

    “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.

  11. Daniyel 9:8kusan 538 K.H.

    Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.

  12. Daniyel 9:9kusan 538 K.H.

    Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

  13. Daniyel 9:10kusan 538 K.H.

    ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.

  14. Daniyel 9:11kusan 538 K.H.

    Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.

  15. Daniyel 9:12kusan 538 K.H.

    Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.

  16. Daniyel 9:13kusan 538 K.H.

    Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.

  17. Daniyel 9:14kusan 538 K.H.

    Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.

  18. Daniyel 9:15kusan 538 K.H.

    “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.

  19. Daniyel 9:16kusan 538 K.H.

    Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.

  20. Daniyel 9:17kusan 538 K.H.

    “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango.

  21. Daniyel 9:18kusan 538 K.H.

    Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka.

  22. Daniyel 9:19kusan 538 K.H.

    Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.”

  23. Daniyel 9:20kusan 538 K.H.

    Yayinda da nake magana da addu’a, ina furta zunubina da zunubin mutanena Isra’ila ina miƙa koke-kokena ga Ubangiji Allahna saboda tudunsa mai tsarki,

  24. Daniyel 9:21kusan 538 K.H.

    yayinda nake cikin addu’a, sai Jibra’ilu, mutumin nan da na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta yamma.

  25. Daniyel 9:22kusan 538 K.H.

    Ya umarce ni ya kuma ce mini, “Daniyel, yanzu na zo domin in ba ka hikima da ganewa.