- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 605–538 BC
The Babylonian Exile
Jerusalem falls and the temple burns; Ezekiel and Daniel minister among the exiles as Lamentations mourns the city's ruin.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Daniyel 7:28kusan 555 K.H.
“Wannan shi ne ƙarshen batun. Ni, Daniyel na damu ƙwarai da irin tunanina, kuma fuskata ta rikice, amma na riƙe batun a zuciyata.”
- Daniyel 8:1kusan 553 K.H.
A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani.
- Daniyel 8:2kusan 553 K.H.
A cikin wahayin, na ga kaina a mafakar Shusha a yankin Elam; a wahayin na ga ina a bakin Kogin Ulai.
- Daniyel 8:3kusan 553 K.H.
Na ɗaga ido, a gabana kuwa sai ga rago mai ƙahoni biyu, yana tsaye a gefen mashigin kogin, ƙahonin kuma suna da tsawo. Ɗaya daga cikin ƙahonin ya fi ɗayan tsawo. Wanda ya fi tsawon shi ne ya tsiro daga baya.
- Daniyel 8:4kusan 553 K.H.
Na lura da ragon sa’ad da ya kai karo wajen yamma da arewa da kudu. Babu wata dabbar da ta iya ƙarawa da shi, babu kuma wanda ya iya kuɓuta daga ikonsa. Ya yi yadda ya ga dama, ya kuma zama mai girma.
- Daniyel 8:5kusan 553 K.H.
Yayinda nake tunani game da wannan, farat ɗaya sai ga bunsurun da yake da sanannen ƙaho tsakanin idanunsa ya ɓullo daga wajen yamma, yana ratsa dukan duniya ba ya ko taɓa ƙasa.
- Daniyel 8:6kusan 553 K.H.
Ya zo wajen rago mai ƙahoni biyu ɗin nan da na riga na gani tsaye a gefen mashigin kogin nan ya tasar masa da fushi mai zafi.
- Daniyel 8:7kusan 553 K.H.
Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, ya kai wa ragon hari. Ya kakkarya ƙahoninsa nan biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, bai iya kāre kansa daga bunsurun ba. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.
- Daniyel 8:8kusan 553 K.H.
Bunsurun kuwa ya ƙasaita, amma a ƙwanƙolin ikonsa sai aka karye babban ƙahonsa, kuma a wurin da ƙahon nan ya kasance waɗansu sanannun ƙahoni huɗu suka tsiro suna fuskantar kusurwoyin nan huɗu.
- Daniyel 8:9kusan 553 K.H.
Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa.
- Daniyel 8:10kusan 553 K.H.
Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su.
- Daniyel 8:11kusan 553 K.H.
Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa.
- Daniyel 8:12kusan 553 K.H.
Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.
- Daniyel 8:13kusan 553 K.H.
Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?”
- Daniyel 8:14kusan 553 K.H.
Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.”
- Daniyel 8:15kusan 553 K.H.
Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum.
- Daniyel 8:16kusan 553 K.H.
Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.”
- Daniyel 8:17kusan 553 K.H.
Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.”
- Daniyel 8:18kusan 553 K.H.
Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye.
- Daniyel 8:19kusan 553 K.H.
Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.
- Daniyel 8:20kusan 553 K.H.
Rago mai ƙahoni biyu da ka gani, yana a madadin sarakunan Medes da Farisa ne.
- Daniyel 8:21kusan 553 K.H.
Bunsurun kuwa sarkin Girka ne, kuma babban ƙahon da yake tsakanin idanunsa, sarki na farko ne.
- Daniyel 8:22kusan 553 K.H.
Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba.
- Daniyel 8:23kusan 553 K.H.
“Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito.
- Daniyel 8:24kusan 553 K.H.
Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka.