- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 7:19kusan 1490 K.H.
“ ‘Ba za a ci naman da ya taɓa wani abu marar tsarki ba; dole a ƙone shi. Game da sauran nama, kowa da yake mai tsarki zai iya ci.
- Firistoci 7:20kusan 1490 K.H.
Amma in wani wanda ba shi da tsarki ya ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
- Firistoci 7:21kusan 1490 K.H.
Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a fid da mutumin daga cikin mutanensa.’ ”
- Firistoci 7:22kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 7:23kusan 1490 K.H.
“Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Kada ku ci wani kitsen shanu, ko na tumaki, ko kuwa na awaki.
- Firistoci 7:24kusan 1490 K.H.
Za a iya yin wani amfani da kitsen dabbar da ta mutu mushe, ko kitsen dabbar da namun jeji su yayyaga, amma kada a kuskura a ci.
- Firistoci 7:25kusan 1490 K.H.
Duk wanda ya ci kitsen dabbar da aka miƙa ta wuta ga Ubangiji, za a fid da shi daga mutanensa.
- Firistoci 7:26kusan 1490 K.H.
Kuma duk inda kuke zama, ba za ku ci jinin wani tsuntsu ko na dabba ba.
- Firistoci 7:27kusan 1490 K.H.
Duk wanda ya ci jini, za a fid da mutumin daga mutanensa.’ ”
- Firistoci 7:28kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 7:29kusan 1490 K.H.
“Faɗa wa Isra’ilawa, ‘Duk wanda ya kawo hadaya ta salama ga Ubangiji, sai ya kawo hadayarsa ga Ubangiji daga cikin hadayu na salama.
- Firistoci 7:30kusan 1490 K.H.
Da hannuwansa zai kawo hadayar da za a ƙona ga Ubangiji; zai kawo kitsen tare da ƙirjin, yă kuma kaɗa ƙirjin a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
- Firistoci 7:31kusan 1490 K.H.
Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza.
- Firistoci 7:32kusan 1490 K.H.
Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko.
- Firistoci 7:33kusan 1490 K.H.
Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa.
- Firistoci 7:34kusan 1490 K.H.
Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”
- Firistoci 7:35kusan 1490 K.H.
Wannan shi ne sashen hadayar da aka ba wa Haruna da ’ya’yansa maza, hadayar da aka yi ga Ubangiji da wuta, tun ranar da aka gabatar da su don su yi wa Ubangiji hidima a matsayin firist.
- Firistoci 7:36kusan 1490 K.H.
A ranar da aka keɓe su, Ubangiji ya umarta cewa Isra’ilawa su ba da wannan a gare su a matsayin rabonsu na kullum, a dukan tsararraki masu zuwa.
- Firistoci 7:37kusan 1490 K.H.
Waɗannan su ne ƙa’idodi don hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, hadaya don zunubi, hadaya don laifi, hadaya ta naɗi da kuma hadaya ta salama,
- Firistoci 7:38kusan 1490 K.H.
waɗanda Ubangiji ya ba wa Musa a Dutsen Sinai, a Hamadar Sinai, a ranar da ya umarci Isra’ilawa su kawo hadayunsu ga Ubangiji.
- Firistoci 8:1kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 8:2kusan 1490 K.H.
“Kawo Haruna da ’ya’yansa maza, ka ɗauki rigunansu, man keɓewa, bijimi domin hadaya don zunubi, ’yan raguna biyu da kuma kwandon da yake da burodi marar yisti,
- Firistoci 8:3kusan 1490 K.H.
ka kuma tara dukan jama’a a ƙofar Tentin Sujada.”
- Firistoci 8:4kusan 1490 K.H.
Sai Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarce shi, jama’a kuwa suka taru a ƙofar Tentin Sujada.
- Firistoci 8:5kusan 1490 K.H.
Sai Musa ya ce wa jama’ar, “Ga abin da Ubangiji ya umarta a yi.”