- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Firistoci 6:24kusan 1490 K.H.
Ubangiji ya ce wa Musa,
- Firistoci 6:25kusan 1490 K.H.
“Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi domin hadaya don zunubi. Za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji a inda ake yankan hadaya ta ƙonawa; dole tă kasance mai tsarki.
- Firistoci 6:26kusan 1490 K.H.
Firist da ya miƙa ta zai ci, za a ci ta a tsattsarkan wuri, a harabar Tentin Sujada.
- Firistoci 6:27kusan 1490 K.H.
Duk abin da ya taɓa wani sashe na naman, zai zama da tsarki, kuma in wani jini ya ɗiga a riga, dole ka wanke shi a tsattsarkan wuri.
- Firistoci 6:28kusan 1490 K.H.
Dole a farfashe tukunyar lakar da aka dafa naman a ciki; amma in an dafa a tukunyar tagulla, sai a kankare tukunyar, a kuma ɗauraye da ruwa.
- Firistoci 6:29kusan 1490 K.H.
Kowane namiji a iyalin firistoci zai iya ci; gama abu ne mafi tsarki.
- Firistoci 6:30kusan 1490 K.H.
Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum.
- Firistoci 7:1kusan 1490 K.H.
“ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodi na hadaya don laifi, hadaya ce tsattsarka.
- Firistoci 7:2kusan 1490 K.H.
Za a yanka hadaya don laifi a inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, za a kuma yayyafa jinin a kowane gefe na bagade.
- Firistoci 7:3kusan 1490 K.H.
Za a miƙa kitsen abin hadaya duka, da wutsiya mai kitse, da kitsen da yake rufe da kayan ciki,
- Firistoci 7:4kusan 1490 K.H.
da ƙodoji biyu da kitsen da yake a bisansu kusa da kwiɓi, da kuma rufin hanta, wanda za a cire tare da ƙodoji.
- Firistoci 7:5kusan 1490 K.H.
Firist zai ƙone su a kan bagade, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji. Hadaya ce don laifi.
- Firistoci 7:6kusan 1490 K.H.
Kowane da namiji cikin iyalin firistoci zai iya ci. Sai a tsattsarkan wuri ne za a ci; gama abu mafi tsarki ne.
- Firistoci 7:7kusan 1490 K.H.
“ ‘Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ƙa’ida hanyar yinsu iri ɗaya ce. Su ɗin na firist da ya yi kafara da su ne.
- Firistoci 7:8kusan 1490 K.H.
Firist da ya miƙa hadaya ta ƙonawa domin wani, zai iya ajiye fatar wa kansa.
- Firistoci 7:9kusan 1490 K.H.
Kowace hadaya ta garin da aka toya a tanda, ko aka dafa a tukunya ko a kan kaskon tuya, na firist da ya miƙa ta ne,
- Firistoci 7:10kusan 1490 K.H.
kuma kowace hadaya ta gari wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, ita ma, ta dukan ’ya’ya Haruna ne maza.
- Firistoci 7:11kusan 1490 K.H.
“ ‘Waɗannan su ne ƙa’idodin hadaya don zumuncin da mutum zai iya miƙa ga Ubangiji.
- Firistoci 7:12kusan 1490 K.H.
“ ‘In ya miƙa hadayar a matsayin hadaya ta godiya ce, to, zai miƙa ta tare da burodi mai kauri marar yisti, wanda aka kwaɓa da mai, da burodi marar kauri, wanda aka shafa wa mai, da kuma burodi mai kauri da aka yi da gari mai laushi wanda aka kwaɓa sosai da mai.
- Firistoci 7:13kusan 1490 K.H.
Tare da hadayarsa don zumunci ta godiya, zai miƙa dunƙulen burodin da aka yi da yisti.
- Firistoci 7:14kusan 1490 K.H.
Zai kuma kawo ɗaya daga kowace a matsayin hadaya, baiko ne ga Ubangiji. Wannan zai zama na firist da ya yafa jinin hadaya ta salama ne.
- Firistoci 7:15kusan 1490 K.H.
Za a ci wannan nama na hadaya don zumunci ta godiya a ranar da aka miƙa ta, kada yă bar wani abu daga naman yă kwana.
- Firistoci 7:16kusan 1490 K.H.
“ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari.
- Firistoci 7:17kusan 1490 K.H.
Duk naman hadayar da ya rage har kwana uku, dole a ƙone shi.
- Firistoci 7:18kusan 1490 K.H.
Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi.