Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 30:16kusan 1491 K.H.

    Ku karɓi kuɗin kafara daga hannun Isra’ilawa, ku yi amfani da shi domin hidimar Tentin Sujada. Zai zama abin tunawa ga Isra’ilawa a gaban Ubangiji, don su yi kafarar rayukansu.”

  2. Fitowa 30:17kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  3. Fitowa 30:18kusan 1491 K.H.

    “Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki.

  4. Fitowa 30:19kusan 1491 K.H.

    Haruna da ’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa.

  5. Fitowa 30:20kusan 1491 K.H.

    Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta,

  6. Fitowa 30:21kusan 1491 K.H.

    za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”

  7. Fitowa 30:22kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  8. Fitowa 30:23kusan 1491 K.H.

    “Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi,

  9. Fitowa 30:24kusan 1491 K.H.

    shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun.

  10. Fitowa 30:25kusan 1491 K.H.

    Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki.

  11. Fitowa 30:26kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari,

  12. Fitowa 30:27kusan 1491 K.H.

    da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare,

  13. Fitowa 30:28kusan 1491 K.H.

    bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa.

  14. Fitowa 30:29kusan 1491 K.H.

    Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki.

  15. Fitowa 30:30kusan 1491 K.H.

    “Ka shafe Haruna da ’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci.

  16. Fitowa 30:31kusan 1491 K.H.

    Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara.

  17. Fitowa 30:32kusan 1491 K.H.

    Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki.

  18. Fitowa 30:33kusan 1491 K.H.

    Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”

  19. Fitowa 30:34kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai.

  20. Fitowa 30:35kusan 1491 K.H.

    Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke.

  21. Fitowa 30:36kusan 1491 K.H.

    Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku.

  22. Fitowa 30:37kusan 1491 K.H.

    Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji.

  23. Fitowa 30:38kusan 1491 K.H.

    Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.”

  24. Fitowa 31:1kusan 1491 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

  25. Fitowa 31:2kusan 1491 K.H.

    “Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,