Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 31:3kusan 1491 K.H.

    na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a,

  2. Fitowa 31:4kusan 1491 K.H.

    don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla,

  3. Fitowa 31:5kusan 1491 K.H.

    don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.

  4. Fitowa 31:6kusan 1491 K.H.

    Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.

  5. Fitowa 31:7kusan 1491 K.H.

    Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin,

  6. Fitowa 31:8kusan 1491 K.H.

    tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare,

  7. Fitowa 31:9kusan 1491 K.H.

    bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa,

  8. Fitowa 31:10kusan 1491 K.H.

    da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan ’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci,

  9. Fitowa 31:11kusan 1491 K.H.

    da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”

  10. Fitowa 31:12kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  11. Fitowa 31:13kusan 1491 K.H.

    “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.

  12. Fitowa 31:14kusan 1491 K.H.

    “ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane.

  13. Fitowa 31:15kusan 1491 K.H.

    Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi.

  14. Fitowa 31:16kusan 1491 K.H.

    Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari.

  15. Fitowa 31:17kusan 1491 K.H.

    Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ”

  16. Fitowa 31:18kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.

  17. Fitowa 32:1kusan 1491 K.H.

    Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.”

  18. Fitowa 32:2kusan 1491 K.H.

    Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.”

  19. Fitowa 32:3kusan 1491 K.H.

    Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna.

  20. Fitowa 32:4kusan 1491 K.H.

    Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”

  21. Fitowa 32:5kusan 1491 K.H.

    Da Haruna ya ga haka, sai ya gina bagade a gaban ɗan maraƙi, ya yi shela ya ce, “Gobe akwai biki ga Ubangiji.”

  22. Fitowa 32:6kusan 1491 K.H.

    Saboda haka kashegari, mutane suka tashi da sassafe suka miƙa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Bayan haka suka zauna suka ci, suka sha, suka kuma tashi suka yi rawa.

  23. Fitowa 32:7kusan 1491 K.H.

    Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu.

  24. Fitowa 32:8kusan 1491 K.H.

    Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”

  25. Fitowa 32:9kusan 1491 K.H.

    Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.”