Tsallake zuwa abun ciki

circa 1446 BC

Sinai & The Law

God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.

1,657 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Fitowa 29:12kusan 1491 K.H.

    Ka ɗibi jinin bijimin ka zuba a kan ƙahoni na bagade da yatsanka, sauran jinin kuwa ka zuba a gindin bagaden.

  2. Fitowa 29:13kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka ɗauki dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake manne da hanta, da ƙoda biyu da kuma kintsen da yake a kansu, ka ƙone su a kan bagade.

  3. Fitowa 29:14kusan 1491 K.H.

    Amma ka ƙone naman bijimin, da fatarsa, da kayan cikin, a bayan sansani. Hadaya ce ta zunubi.

  4. Fitowa 29:15kusan 1491 K.H.

    “Ka ɗauki ɗaya daga cikin ragunan, Haruna kuwa da ’ya’yan maza za su ɗora hannuwansa a kansa.

  5. Fitowa 29:16kusan 1491 K.H.

    Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.

  6. Fitowa 29:17kusan 1491 K.H.

    Ka yayyanka rago gunduwa-gunduwa, ka wanke kayan cikin, da ƙafafun, da kan, ka haɗa su da gunduwoyin.

  7. Fitowa 29:18kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka ƙone ragon ɗungum a kan bagade. Hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  8. Fitowa 29:19kusan 1491 K.H.

    “Ka ɗauki ɗayan ragon, sai Haruna da ’ya’yansa maza su ɗora hannuwansu a kansa.

  9. Fitowa 29:20kusan 1491 K.H.

    Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.

  10. Fitowa 29:21kusan 1491 K.H.

    Ka ɗibi jinin da yake a kan bagade, da man shafewa, ka yafa a kan Haruna da rigunansa, da kuma a kan ’ya’yansa maza da rigunansu. Sa’an nan shi da ’ya’yansa maza da rigunansu za su tsarkake.

  11. Fitowa 29:22kusan 1491 K.H.

    “Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)

  12. Fitowa 29:23kusan 1491 K.H.

    Daga kwandon burodi marar yisti, wanda yake gaban Ubangiji, ka ɗauki dunƙule ɗaya, da waina da aka yi da mai, da kuma ƙosai.

  13. Fitowa 29:24kusan 1491 K.H.

    Ka sa dukan waɗannan a hannun Haruna da ’ya’yansa maza, su kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.

  14. Fitowa 29:25kusan 1491 K.H.

    Sa’an nan ka karɓe su daga hannuwansu, ka ƙone su a kan bagade tare da hadaya ta ƙonawa, domin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

  15. Fitowa 29:26kusan 1491 K.H.

    Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.

  16. Fitowa 29:27kusan 1491 K.H.

    “Ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa, waɗanda za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon naɗin, wanda yake na Haruna da kuma na ’ya’yansa maza.

  17. Fitowa 29:28kusan 1491 K.H.

    Wannan zai zama rabon Haruna da ’ya’yansa maza daga Isra’ilawa. Gama wannan hadaya ta ɗagawa ce daga cikin hadayu na salama da Isra’ilawa za su miƙa wa Ubangiji.

  18. Fitowa 29:29kusan 1491 K.H.

    “Keɓaɓɓun tufafin nan na Haruna za su zama na zuriyarsa bayan mutuwarsa. Da tufafin nan ne za a zuba musu mai, a keɓe su.

  19. Fitowa 29:30kusan 1491 K.H.

    Ɗan da ya gāje shi a matsayin firist, shi ne zai sa su har kwana bakwai, lokacin da ya shiga Tentin Sujada, don yă yi aiki a Wuri Mai Tsarki.

  20. Fitowa 29:31kusan 1491 K.H.

    “Ka ɗauki ragon naɗi, ka dafa naman a tsattsarkan wuri.

  21. Fitowa 29:32kusan 1491 K.H.

    A ƙofar Tentin Sujada, Haruna da ’ya’yansa maza za su ci wannan rago da burodin da yake cikin kwandon.

  22. Fitowa 29:33kusan 1491 K.H.

    Za su ci abubuwan nan da aka yi kafara da su a lokacin tsarkakewarsu da keɓewarsu. Ba wanda zai ci, sai su kaɗai, gama abubuwan nan tsarkaka ne.

  23. Fitowa 29:34kusan 1491 K.H.

    In naman ragon naɗi ko wani burodin ya ragu har safiya, a ƙone shi, kada a ci gama tsarkake ne.

  24. Fitowa 29:35kusan 1491 K.H.

    “Ka yi wa Haruna da ’ya’yansa maza duk abin da na umarce ka, ka ɗauki kwana bakwai don naɗinsu.

  25. Fitowa 29:36kusan 1491 K.H.

    Ka miƙa bijimi ɗaya kowace rana domin hadaya don zunubi ta yin kafara. Ka tsarkake bagade ta wuri yin kafara dominsa, ka shafe shi da mai don ka tsarkake shi.