- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1446 BC
Sinai & The Law
God meets Israel at Mount Sinai, reveals the Ten Commandments, and establishes the Tabernacle and the priestly covenant.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Fitowa 28:30kusan 1491 K.H.
Ka kuma sa Urim da Tummim a ƙyallen maƙalawa a ƙirji, don su kasance a zuciyar Haruna, a duk sa’ad da zai shiga gaban Ubangiji. Haka kuwa kullum Haruna zai riƙa kai koke-koken Isra’ilawa a gaban Ubangiji.
- Fitowa 28:31kusan 1491 K.H.
“Ka yi taguwar efod da shuɗi duka,
- Fitowa 28:32kusan 1491 K.H.
ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage.
- Fitowa 28:33kusan 1491 K.H.
Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin ’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu.
- Fitowa 28:34kusan 1491 K.H.
Za ka jera su bi da bi, wato, ’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar.
- Fitowa 28:35kusan 1491 K.H.
Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu.
- Fitowa 28:36kusan 1491 K.H.
“Ka yi allo na zinariya zalla, ka kuma yi rubutu a kansa kamar na hatimi, haka, Mai tsarki ga Ubangiji.
- Fitowa 28:37kusan 1491 K.H.
Ka ɗaura shi da igiyar ruwa bula domin a haɗa shi da rawani; zai kasance a gaban rawanin.
- Fitowa 28:38kusan 1491 K.H.
Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji.
- Fitowa 28:39kusan 1491 K.H.
“Ka saƙa doguwar riga da lallausan lilin ka kuma yi hula da lallausan zaren lilin, ka kuma saƙa abin ɗamara mai ado.
- Fitowa 28:40kusan 1491 K.H.
“Ka saƙa doguwar riga, abin ɗamara da kuma huluna domin ’ya’yan Haruna, don yă ba su girma da ɗaukaka.
- Fitowa 28:41kusan 1491 K.H.
Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da ’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.
- Fitowa 28:42kusan 1491 K.H.
“Ka yi ’yan wandunan ciki na lilin don su rufe tsiraicinsu, tsayinsu zai kama daga kwankwaso zuwa cinya.
- Fitowa 28:43kusan 1491 K.H.
Dole Haruna da ’ya’yansa su sa su sa’ad da za su shiga Tentin Sujada, ko sa’ad da suka kusace bagade domin hidima a Wuri Mai Tsarki, don kada su yi laifi, su kuma mutu. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa Haruna da zuriyarsa har abada.
- Fitowa 29:1kusan 1491 K.H.
“Ga abin da za ka yi don ka keɓe su, don su yi mini hidima a matsayin firistoci. Ka ɗauki ɗan bijimi da raguna biyu marasa lahani.
- Fitowa 29:2kusan 1491 K.H.
Daga garin alkama mai laushi marar yisti kuwa, ka yi burodi, da wainan da aka kwaɓa da mai, da ƙosai waɗanda an barbaɗa mai a kai.
- Fitowa 29:3kusan 1491 K.H.
Ka sa waɗannan a cikin kwando. Sa’an nan ka miƙa su tare da ɗan bijimin da ragunan nan biyu.
- Fitowa 29:4kusan 1491 K.H.
Bayan haka sai ka kawo Haruna da ’ya’yansa a ƙofar Tentin Sujada ka yi musu wanka.
- Fitowa 29:5kusan 1491 K.H.
Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado.
- Fitowa 29:6kusan 1491 K.H.
Ka naɗa masa rawani a kai, ka kuma sa kambi mai tsarki a bisa rawanin.
- Fitowa 29:7kusan 1491 K.H.
Ka ɗauki man shafewa ka shafe shi, ta wurin zuba man a kansa.
- Fitowa 29:8kusan 1491 K.H.
Ka kawo ’ya’yansa, ka sa musu taguwoyi,
- Fitowa 29:9kusan 1491 K.H.
ka kuma sa musu huluna a kansu. Sa’an nan ka ɗaura wa Haruna da ’ya’yansa abin ɗamara. Su kuwa da zuriyarsu, aikin firist kuwa zai zama nasu ta wurin dawwammamiyar farilla. “Ta haka za ka keɓe Haruna da ’ya’yansa maza.
- Fitowa 29:10kusan 1491 K.H.
“Ka kuma kawo bijimin a gaban Tentin Sujada, sai Haruna da ’ya’yansa su ɗora hannuwansu a kansa.
- Fitowa 29:11kusan 1491 K.H.
Ka yanka shi a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada.