circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Timoti 3:3kusan 66 M.
marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta,
- 2 Timoti 3:4kusan 66 M.
masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah
- 2 Timoti 3:5kusan 66 M.
suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
- 2 Timoti 3:6kusan 66 M.
Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu,
- 2 Timoti 3:7kusan 66 M.
kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.
- 2 Timoti 3:8kusan 66 M.
Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.
- 2 Timoti 3:9kusan 66 M.
Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.
- 2 Timoti 3:10kusan 66 M.
Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri,
- 2 Timoti 3:11kusan 66 M.
tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu.
- 2 Timoti 3:12kusan 66 M.
Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
- 2 Timoti 3:13kusan 66 M.
Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.
- 2 Timoti 3:14kusan 66 M.
Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su,
- 2 Timoti 3:15kusan 66 M.
da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
- 2 Timoti 3:16kusan 66 M.
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,
- 2 Timoti 3:17kusan 66 M.
domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
- 2 Timoti 4:1kusan 66 M.
A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni.
- 2 Timoti 4:2kusan 66 M.
Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa.
- 2 Timoti 4:3kusan 66 M.
Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.
- 2 Timoti 4:4kusan 66 M.
Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.
- 2 Timoti 4:5kusan 66 M.
Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.
- 2 Timoti 4:6kusan 66 M.
Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi.
- 2 Timoti 4:7kusan 66 M.
Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.
- 2 Timoti 4:8kusan 66 M.
Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
- 2 Timoti 4:9kusan 66 M.
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri,
- 2 Timoti 4:10kusan 66 M.
gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.