Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Bitrus 2:7kusan 60 M.

    A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini,

  2. 1 Bitrus 2:8kusan 60 M.

    kuma, “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe kuma fā ne da yake sa su fāɗi.” Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

  3. 1 Bitrus 2:9kusan 60 M.

    Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  4. 1 Bitrus 2:10kusan 60 M.

    Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.

  5. 1 Bitrus 2:11kusan 60 M.

    Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.

  6. 1 Bitrus 2:12kusan 60 M.

    Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

  7. 1 Bitrus 2:13kusan 60 M.

    Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko,

  8. 1 Bitrus 2:14kusan 60 M.

    ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai.

  9. 1 Bitrus 2:15kusan 60 M.

    Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci.

  10. 1 Bitrus 2:16kusan 60 M.

    Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah.

  11. 1 Bitrus 2:17kusan 60 M.

    Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

  12. 1 Bitrus 2:18kusan 60 M.

    Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma.

  13. 1 Bitrus 2:19kusan 60 M.

    Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah.

  14. 1 Bitrus 2:20kusan 60 M.

    Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah.

  15. 1 Bitrus 2:21kusan 60 M.

    Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

  16. 1 Bitrus 2:22kusan 60 M.

    “Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.”

  17. 1 Bitrus 2:23kusan 60 M.

    Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.

  18. 1 Bitrus 2:24kusan 60 M.

    Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.

  19. 1 Bitrus 2:25kusan 60 M.

    Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.

  20. 1 Bitrus 3:1kusan 60 M.

    Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba

  21. 1 Bitrus 3:2kusan 60 M.

    sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.

  22. 1 Bitrus 3:3kusan 60 M.

    Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada.

  23. 1 Bitrus 3:4kusan 60 M.

    Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.

  24. 1 Bitrus 3:5kusan 60 M.

    Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,

  25. 1 Bitrus 3:6kusan 60 M.

    kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.