Tsallake zuwa abun ciki

Egypt

561 verses · 4 known names

An kuma san shi da: Egyptian, Egyptians, Egyptian's

30.1000, 31.3300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Egypt

Tace bisa littafi
  1. “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.

  2. Zan sa jama’arka su mutu ta wurin takuban ƙarfafan mutane, masu bantsoro na dukan al’ummai. Za su lalatar da girman kan Masar, su kuma tumɓuke dukan jama’arta.

  3. Sa’ad da na mai da Masar kufai na kuma raba ƙasar da abin da take cike da shi, sa’ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta, a sa’an nan ne za su san cewa ni ne Ubangiji.’

  4. “Wannan ne makokin da za a yi mata. ’Yan matan al’ummai za su rera shi; gama Masar da dukan jama’arta za su rera shi, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  5. “Ɗan mutum, yi kuka saboda jama’ar Masar ka kuma tura ta da ’yan matan manyan al’ummai zuwa ƙarƙashin ƙasa, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

  6. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.

  7. Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba.

  8. Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba.

  9. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi.

  10. A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.

  11. “Efraim yana kama da kurciya, marar wayo, marar hankali, yanzu yana kira ga Masar, yanzu yana juyewa ga Assuriya.

  12. Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka; suna kama da tanƙwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi saboda banzan maganganunsu. Saboda wannan za a wulaƙanta su a ƙasar Masar.

  13. Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar.

  14. Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.

  15. Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.

  16. “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi, daga Masar kuma na kira ɗana.

  17. “Ba za su koma Masar ba Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba saboda sun ƙi su tuba ba?

  18. Za su zo da rawan jiki kamar tsuntsaye daga Masar, kamar kurciyoyi daga Assuriya. Zan zaunar da su a cikin gidajensu,” in ji Ubangiji.

  19. Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.

  20. “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.

  21. Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.

  22. “Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni.

  23. Amma Masar za tă zama kango, Edom kuma hamada marar amfani, saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.

  24. Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.

  25. Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.