Tsallake zuwa abun ciki

Babylon

255 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Babylon's, Sheshach

32.5300, 44.4200 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Babylon

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Takobin sarkin Babilon zai auko maka.

  2. A Shekara ta uku ta mulki Yehohiyakim sarkin Yahuda, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya zo Urushalima ya kuma yi mata ƙawanya.

  3. Wannan ya sa sarki ya fusata ƙwarai, ya ba da umarni a tafi da dukan masu hikima na Babilon a kashe su.

  4. Sa’ad da Ariyok, shugaban ƙungiyar matsaran sarki, ya fita domin yă kashe masu hikima na Babilon, sai Daniyel ya yi masa magana cikin hikima da dabara.

  5. Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon.

  6. Sai Daniyel ya tafi wurin Ariyok, wanda sarki ya sa yă kashe masu hikiman Babilon, ya kuma ce masa, “Kada ka kashe masu hikiman Babilon ka kai ni wurin sarki, ni kuma zan fassara masa mafarkinsa.”

  7. Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima.

  8. Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.

  9. Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon.

  10. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.”

  11. Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.

  12. Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin.

  13. Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon,

  14. sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?”

  15. Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”

  16. A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa.

  17. Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.

  18. “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!”

  19. “Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya.

  20. Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.

  21. Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,

  22. Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.

  23. Kun ɗaukaka gidan tsafin Molek, da tauraron allahnku Refan, gumakan da kuka ƙera don ku yi musu sujada. Saboda haka zan aike ku zuwa bauta’ gaba da Babilon.

  24. Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus.

  25. Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”