Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.

  2. Allah ne fa yake sa mu da ku mu tsaya daram cikin Kiristi. Shi ne ya shafe mu,

  3. In kuka gafarta wa wani, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta kuwa, in har ma da abin gafartawa, saboda ku ne na gafarta masa, albarkacin Kiristi,

  4. To, sa’ad da na tafi Toruwas don in yi wa’azin bisharar Kiristi, ko da yake na tarar cewa Ubangiji ya buɗe mini ƙofa,

  5. Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina.

  6. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka.

  7. Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

  8. Kun nuna cewa ku wasiƙa ce daga Kiristi, sakamakon hidimarmu, ba wadda aka rubuta da inki ba, sai dai da Ruhun Allah mai rai. Ba kuma a kan allunan dutse ba, sai dai a kan allunan zukatan mutane.

  9. Amincewa kamar wannan shi ne namu ta wurin Kiristi a gaban Allah.

  10. Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi.

  11. Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin.

  12. Ubangiji fa, shi ne Ruhu, kuma duk inda Ruhun Ubangiji yake, a nan ’yanci yake.

  13. Mu da ba mu da lulluɓi a fuskokinmu duk muna nuna ɗaukakar Ubangiji, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji wanda yake ruhu kuwa shi ne mai zartar da haka.

  14. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah.

  15. Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.

  16. Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.

  17. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu.

  18. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.

  19. Domin mun san cewa shi da ya tā da Ubangiji Yesu daga matattu, zai tashe mu mu ma tare da Kiristi, yă kuma miƙa mu a gabansa tare da ku.

  20. Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.

  21. Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji.

  22. Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji.

  23. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.

  24. Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.

  25. To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.