Tsallake zuwa abun ciki

Jesus

3,872 ayoyi · 6 'yan gida

An kuma san shi da: Jesus Christ, Immanuel, Emmanuel, Christ

Ayoyin da suka ambaci Jesus

Tace bisa littafi
  1. Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.

  2. Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.

  3. Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa.

  4. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.

  5. Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  6. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.

  7. Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.

  8. Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  9. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito.

  10. Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  11. Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

  12. A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.

  13. Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi ’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.

  14. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.

  15. Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.

  16. Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!

  17. Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.

  18. Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.

  19. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, tare da dukan tsarkaka a ko’ina a Akayya.

  20. Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

  21. Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya,

  22. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba.

  23. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,

  24. kamar yadda kuka ɗan fahimce mu, za ku kai ga cikakkiyar fahimta cewa za ku iya yin taƙama da mu, kamar yadda mu ma za mu yi taƙama da ku a ranar da Ubangiji Yesu zai dawo.

  25. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.