Tsallake zuwa abun ciki

Israel

1,007 ayoyi · 20 'yan gida

An kuma san shi da: Jacob

Ayoyin da suka ambaci Israel

Tace bisa littafi
  1. Saboda sunan Yaƙub bawana, Isra’ila zaɓaɓɓena, na kira ka da suna na ba ka matsayin bangirma, ko da yake ba ka san ni ba.

  2. Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai.

  3. “Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.

  4. “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba,

  5. “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.

  6. Ku bar Babilon, ku gudu daga Babiloniyawa! Ku yi shelar wannan da sowa ta farin ciki ku kuma furta shi. Ku aika shi zuwa iyakokin duniya; ku ce, “Ubangiji ya fanshi bawansa Yaƙub.”

  7. Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina

  8. ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”

  9. Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”

  10. “Ku yi ihu da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa. Ku tā da muryarku kamar busar ƙaho. Ku furta wa mutanena tawayensu da kuma ga gidan Yaƙub zunubansu.

  11. sa’an nan za ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, zan kuma sa ku a kan maɗaukaka ƙasashe ku kuma yi biki a gādon mahaifinku Yaƙub.” Ni Ubangiji ne na faɗa.

  12. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.

  13. Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.

  14. Zan fitar da zuriyar Yaƙub, daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna; zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su, a can kuma bayina za su zauna.

  15. Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.

  16. Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub, dukanku zuriyar gidan Isra’ila.

  17. An ji kuka a filayen tuddai, kuka da roƙon mutanen Isra’ila, domin sun lalace hanyoyinsu sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.

  18. “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda.

  19. Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba, gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka, har da Isra’ila, kabilar gādonsa Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  20. Ka zuba hasalarka a kan al’umman da ba su san ka ba, a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka. Gama sun cinye Yaƙub; sun cinye shi gaba ɗaya suka kuma lalace wurin zamansa.

  21. “Amma fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “da mutane ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga Masar,’

  22. amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashe da ya kora su.’ Gama zan komo da su zuwa ƙasar da na ba wa kakanninsu.

  23. “Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’

  24. Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.

  25. “ ‘Saboda haka kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana; kada ka karai, ya Isra’ila,’ in ji Ubangiji. ‘Tabbatacce zan cece ka daga wuri mai nesa, zuriyarka daga ƙasar zaman bautansu. Yaƙub zai sami salama da zaman lafiya, kuma ba wanda zai sa ya ji tsoro.