God
Ayoyin da suka ambaci God
Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni.
Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,
amma ’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata.
Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da ’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’
“Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!
Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.”
Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa.
Yoshuwa ya ba Kaleb ɗan Yefunne wuri a Yahuda, Kiriyat Arba, wato, Hebron, bisa ga umarnin Ubangiji. (Arba shi ne mahaifin Anak.)
Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.
Mutanen Yusuf kuwa suka ce wa Yoshuwa, “Me ya sa ka ba mu rabon gādo ɗaya kawai? Ga shi muna da yawa kuma Ubangiji ya albarkace mu sosai.”
Saboda haka Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na iyayenku ya ba ku?
Bayan kun auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sai ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuma in yi muku ƙuri’a a gaban Ubangiji Allahnmu.
Lawiyawa ba su da rabo a cikinku, domin aikin firistocin da suke yi wa Ubangiji shi ne gādonsu. Gad, Ruben da rabin kabilar Manasse kuwa sun riga sun samu gādonsu a gabashin gefen Urdun, Musa bawan Ubangiji ya ba su.”
Da mutanen za su kama hanya su je su zāna yadda ƙasar take, Yoshuwa ya umarce su cewa, “Ku je ku ga yadda ƙasar take. Sa’an nan ku dawo wurina, zan yi muku ƙuri’a a nan Shilo a gaban Ubangiji.”
Sai Yoshuwa ya yi musu ƙuri’a a gaban Ubangiji, a nan ne ya raba wa Isra’ilawa ƙasar bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.
yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.
Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.
Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,
“Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa,
Shilo cikin Kan’ana, suka ce musu, “Ubangiji ya yi umarni ta wurin Musa cewa a ba mu garuruwan da za mu zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau don dabbobinmu.”
Saboda haka kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.
Haka Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo masu kyau, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya yi wa kakanninsu alkawari, suka kuwa mallake ta, suka zauna a cikinta.
Ubangiji ya ba su hutawa a kowane gefe kamar yadda ya yi wa kakanninsu alkawari, ba ko ɗaya daga cikin abokan gābansu da ya iya cinsu da yaƙi.