Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu; na ba ka su a hannunka. Ba waninsu da zai iya tsayayya da kai.”

  2. Ubangiji ya sa suka ruɗe a gaban Isra’ilawa, Isra’ilawa kuwa suka yi babbar nasara a kansu a Gibeyon. Isra’ilawa suka fafare su a kan hanyar zuwa Bet-Horon suka karkashe su duka har zuwa Azeka da Makkeda.

  3. Suna guje wa Isra’ilawa suna gangarawa a kan hanyar Bet-Horon har zuwa Azeka, sai Ubangiji ya turo manyan duwatsu daga sararin sama suka karkashe su, waɗanda manyan duwatsun suka kashe sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kashe da takobi.

  4. A ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa a hannun Isra’ilawa, Yoshuwa ya ce wa Ubangiji a gaban Isra’ilawa, “Ke rana, ki tsaya cik a Gibeyon Kai wata, ka je Kwarin Aiyalon.”

  5. Ba a taɓa ganin abu haka ba ko dā can, ranar da Ubangiji ya saurari mutum. Ba shakka Ubangiji yana yaƙi domin Isra’ilawa.

  6. Amma kada ku tsaya a can! Ku fafari abokan gābanku, ku kai musu hari ta baya, kada ku bari su kai biranensu, gama Ubangiji Allahnku ya ba da su a hannunku.”

  7. Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.”

  8. Ubangiji kuma ya ba da ƙasar da sarkinta a hannun Yoshuwa. Yoshuwa ya karkashe kowa ya hallaka birnin, bai bar wani da rai ba. Ya kuma yi wa sarkin yadda ya yi wa sarkin Yeriko.

  9. Ubangiji ya ba da Lakish a hannun Isra’ilawa, a rana ta biyu kuwa Yoshuwa ya ci nasara a kansu. Ya karkashe duk mutanen birnin ya kuma hallaka birnin, kamar yadda ya yi a Libna.

  10. Yoshuwa ya cinye yankin duka da yaƙi, haɗe da na kan tudu, da Negeb, da kwarin yamma, da filayen cikin duwatsu tare da sarakunansu duka. Bai bar wani da rai ba, ya kashe duk wani mai numfashi, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ilawa ya umarta.

  11. Yoshuwa kuwa ya cinye sarakunan nan duka da ƙasashensu gaba ɗaya gama Ubangiji, Allah na Isra’ila ne ya yi yaƙi domin Isra’ilawa.

  12. Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, domin war haka gobe zan ba da dukansu a hannun Isra’ilawa, za su kuwa karkashe su. Za ku gurgunta dawakansu, ku kuma ƙone keken yaƙinsu.”

  13. Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa nasara a kan su, suka ci su da yaƙi, suka fafare su har zuwa Sidon Babba, zuwa Misrefot Mayim, har zuwa Kwarin Mizfa a gabas, ba wanda suka bari da rai.

  14. Yoshuwa ya yi musu yadda Ubangiji ya umarta, ya gurgunta dawakansu, ya kuma ƙone keken yaƙinsu.

  15. Yoshuwa ya ƙwace masarautun nan duka ya kuma kashe sarakunansu da takobi, ya hallakar da su ƙaƙaf kamar yadda Musa bawan Ubangiji ya umarta.

  16. Yadda Ubangiji ya umarci bawansa Musa, haka Musa ya umarci Yoshuwa, shi kuwa ya yi duk abin da Ubangiji ya umarci Musa.

  17. Gama Ubangiji ne ya taurare zukatansu waɗannan sarakuna suka yi yaƙi da Isra’ilawa don yă hallaka su gaba ɗaya, yă gamar da su ba jinƙai, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  18. Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi.

  19. Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

  20. Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.

  21. “Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,

  22. Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.

  23. Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.

  24. Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.

  25. Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.