Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

  2. Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.

  3. Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.

  4. Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”

  5. Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.

  6. A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

  7. Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

  8. Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.

  9. Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”

  10. ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.

  11. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”

  12. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’”

  13. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  14. Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.

  15. Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”

  16. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.

  17. “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!”

  18. Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.

  19. Amma ya ce, “Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”

  20. Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,

  21. Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

  22. Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.

  23. Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”

  24. Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”

  25. Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah.