Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.

  2. Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

  4. wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub.

  5. Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.

  6. Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando.

  7. Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela

  8. “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!

  9. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

  10. “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

  11. Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu.

  12. “A ce mutanena za su saurare ni, a ce Isra’ila zai bi hanyoyina,

  13. da nan da nan sai in rinjayi abokan gābansu in kuma juye hannuna a kan maƙiyansu!

  14. Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.

  15. Amma za a ciyar da ku da alkama mafi kyau; da zuma daga dutsen da zai ƙosar da ku.”

  16. Zabura ta Asaf. Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

  17. “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

  18. Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

  19. Waƙa ce. Zabura ta Asaf. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.

  20. Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.

  21. Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.

  22. Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai,

  23. waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.”

  24. Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa,

  25. haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka.