God
Ayoyin da suka ambaci God
amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.
Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.
Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;
daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa.
Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.
Sun ba da gawawwakin bayinka kamar abinci ga tsuntsayen sararin sama, nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.
Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne? Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?
Ka zuba fushinka a kan al’umman da ba su yarda da kai ba, a kan mulkokin da ba sa kira bisa sunanka;
Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai.
Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
Don me al’ummai za su ce, “Ina Allahnsu yake?” A idanunmu, ka sanar wa al’ummai cewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.
Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.
Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.
Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka
a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.
Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.
Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?
Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.
Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?
Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,
saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.
An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.
Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.