Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.

  2. A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.

  3. Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.

  4. Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;

  5. zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.

  6. Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.

  7. Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.

  8. Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!

  9. Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.

  10. Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,

  11. ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.

  12. Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.

  13. Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.

  14. Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.

  15. Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.

  16. Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.

  17. Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.

  18. Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.

  19. Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.

  20. Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.

  21. Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.

  22. Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.

  23. Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.

  24. Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.

  25. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;