Tsallake zuwa abun ciki

Aaron

331 ayoyi · 9 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Aaron

Tace bisa littafi
  1. Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da ’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  2. Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana

  3. “’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa.

  4. Miriyam da Haruna suka fara zargin Musa saboda matarsa ’yar ƙasar Kush da ya aura.

  5. Nan da nan Ubangiji ya ce wa Musa, da Haruna da kuma Miriyam, “Ku fita ku tafi Tentin Sujada, dukanku uku.” Sai dukansu uku suka tafi.

  6. Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,

  7. Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;

  8. sai Haruna ya ce wa Musa, “Ranka yă daɗe, ina roƙonka kada ka hukunta mu, gama zunubin da muka yi, mun yi ne cikin wauta.

  9. Suka dawo wurin Musa, da Haruna, da dukan jama’ar Isra’ilawa, a Kadesh, a Hamadan Faran. A can suka ba da rahoton ga dukan taron da yake wurin, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar.

  10. Dukan Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, dukan taron kuwa suka ce musu, “Da ma mun mutu a Masar! Ko kuma a wannan hamada ma!

  11. Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban jama’ar Isra’ilawa da suka taru a can.

  12. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  13. Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,

  14. tare kuwa suka zo wurin Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun wuce gona da iri! Dukan jama’an nan masu tsarki ne, kowannensu, Ubangiji kuma yana tare da su. Me ya sa kuke ɗaukan kanku fiye da taron jama’ar Ubangiji?”

  15. Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji.”

  16. Musa ya ce wa Kora, “Da kai da kuma dukan ƙungiyarka za ku bayyana a gaban Ubangiji gobe, kai da su. Haruna ma zai kasance a can.

  17. Kowannenku zai ɗauki faranti yă zuba turare a ciki. Wato, farantai 250 ke nan, a kuma miƙa su a gaban Ubangiji. Kai da Haruna za ku miƙa farantanku, ku ma.”

  18. Sai kowane mutum ya ɗauki farantinsa, ya sa wuta da kuma turare a ciki, suka tsaya da Musa da Haruna a ƙofar Tentin Sujada.

  19. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  20. “Ka gaya wa Eleyazar ɗan Haruna, firist, yă kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, yă watsar da gawayin a wani wuri, gama farantan tsarkakakku ne,

  21. yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa.

  22. Kashegari dukan taron Isra’ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna suka ce, “Kun kashe mutanen Ubangiji.”

  23. Bayan haka, sai dukan jama’a suka taru domin su nuna rashin yardansu da abin da suke zato Musa da Haruna ne suka aikata. Da suka fuskanci Tentin Sujada, nan take sai girgije ya rufe shi, ɗaukaka Ubangiji kuwa ta bayyana.

  24. Sai Musa da Haruna suka je gaban Tentin Sujada,

  25. Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”