Tsallake zuwa abun ciki

Aaron

331 ayoyi · 9 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Aaron

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Haruna ya yi kamar yadda Musa ya faɗa, ya ruga a guje zuwa tsakiyar taron. An riga an fara annobar a cikin mutane, amma Haruna ya miƙa turaren ya kuma yi kafara dominsu.

  2. Sai Haruna ya komo wurin Musa a ƙofar Tentin Sujada, gama annobar ta ƙare.

  3. A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.

  4. Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.

  5. Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon.

  6. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”

  7. Ubangiji ya ce wa Haruna, “Kai da ’ya’yanka, da kuma iyalin mahaifinka za ku ɗauki hakkin abin da ya shafi Tentin Sujada, kai da ’ya’yanka kaɗai za ku ɗauki hakkin aikinku wanda ya shafi firistoci.

  8. Sai Ubangiji ya ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayun da za a miƙa mini, dukan tsarkakan hadayun da Isra’ilawa suka ba ni, na ba ka su su zama rabonka da na ’ya’yanka har abada.

  9. Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa.

  10. Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji.

  11. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  12. Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna.

  13. Sai Musa da Haruna suka tashi daga taron, suka tafi ƙofar Tentin Sujada, suka fāɗi rubda ciki, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana musu.

  14. “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”

  15. Shi da Haruna, suka tara jama’a a gaban dutsen, Musa ya ce musu, “Ku saurara, ku ’yan tawaye, dole mu kawo muku ruwa daga wannan dutse?”

  16. Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”

  17. A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  18. “Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba.

  19. Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor.

  20. Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.”

  21. Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,

  22. sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.

  23. Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi

  24. “Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra’ilawa; saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka saboda ɗaukakata ban kawo ƙarshensu ba.

  25. Bayan annobar, sai Ubangiji ya yi magana da Musa da Eleyazar ɗan Haruna, firist ya ce,