Skip to content
Yoshuwa 19:31-51

Yoshuwa 19:31-51

31
Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
32
Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.
33
Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun.
34
Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
35
Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,
36
Adama, Rama, Hazor,
37
Kedesh, Edireyi, En Hazor,
38
Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.
39
Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.
40
Ƙuri’a ta bakwai ta fāɗa a kan kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
41
Ƙasarsu ta gādo ta haɗa da, Zora, Eshtawol, Ir Shemesh,
42
Shalim, Aiyalon, Itla,
43
Elon, Timna, Ekron,
44
Elteke, Gibbeton, Ba’alat,
45
Yehud, Bene-Berak, Gat-Rimmon,
46
Me Yarkon da Rakkon tare da sashen da yake fuskantar Yaffa.
47
(Amma ya zama wa mutanen kabilar Dan da wahala su mallaki ƙasar da aka ba su gādo, saboda haka sai suka nufi Leshem suka ci su da yaƙi, suka karkashe mutanen wurin, suka mallake ta, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato, Dan.)
48
Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan, bisa ga iyalansu.
49
Sa’ad da aka gama raba gādon ƙasar bisa ga ƙuri’a. Sai Isra’ilawa suka ba Yoshuwa ɗan Nun nasa rabo a cikinsu,
50
yadda Ubangiji ya umarta, suka ba shi garin da ya ce a ba shi, Timnat Serad a ƙasar tudu ta Efraim. Ya kuma gina garin ya zauna a can.
51
Waɗannan su ne rabe-raben gādon da Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin kabilan iyalan Isra’ila suka rarraba ta hanyar jefa ƙuri’a a Shilo a gaban Ubangiji a ƙofar Tentin Sujada. Da haka suka yi suka gama rarraba ƙasar.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options