Yoshuwa 19:24-31
24
Ƙuri’a ta biyar ta fāɗa a kan kabilar Asher, bisa ga iyalansu.
25
Ƙasarsu gādonsu ta haɗa da, Helkat, Hali, Beten, Akshaf,
26
Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.
27
Sai ta yi gabas zuwa Bet-Dagon, ta taɓa Zebulun da kuma Kwarin Ifta El, ta wuce arewa zuwa Bet-Emek da Neyiyel, ta wuce Kabul a hagu,
28
ta kai Abdon, Rehob, Hammon da Kana, har zuwa Sidon Babba.
29
Daga nan iyakar ta juya baya zuwa Rama, ta bi ta birnin nan mai katanga na Taya, ta juya ta nufi Hosa, sa’an nan ta ɓulla ta Bahar Rum cikin yankin Akzib,
30
Umma, Afek da Rehob. Garuruwa ashirin da biyu ke nan da ƙauyukansu.
31
Garuruwan nan da ƙauyukansu su ne gādon da kabilar Asher ta samu bisa ga iyalansu.
Settings