2 Sama’ila 23:13-39
13
A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.
14
Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.
15
Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”
16
Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.
17
Sai ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.
18
Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.
19
Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
20
Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
21
Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.
22
Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.
23
Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
24
Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
25
Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod,
26
Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,
27
Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha,
28
Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa,
29
Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,
30
Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,
31
Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim,
32
Eliyaba, mutumin Sha’albo, ’Ya’yan Yashen, Yonatan,
33
ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.
34
Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,
35
Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,
36
Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri,
37
Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,
38
Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra,
39
da kuma Uriya, mutumin Hitti. Su talatin da bakwai ne duka.
Settings