Skip to content
2 Sama’ila 23:8-12

2 Sama’ila 23:8-12

8
Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
9
Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,
10
amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
11
Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.
12
Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options