Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Simeon: Bounds of their inheritance with cities and villages
Ayoyi game da Bounds of their inheritance with cities and villages
Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,
Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,
Eltolad, Betul, Horma,
Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,
Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.
Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,
da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.
Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,
Bilha, Ezem, Tolad
Betuwel, Horma, Ziklag,
Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.
Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;
da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya.