Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Simeon: Inheritance of, within Judah

8 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Inheritance of, within Judah

  1. Ƙuri’a ta biyu ta fāɗa a kan kabilar Simeyon, bisa ga iyalansu. Ƙasarsu ta gādo tana cikin yankin Yahuda.

  2. Waɗannan su ne wuraren da suka gāda. Beyersheba (ko Sheba), Molada,

  3. Hazar Shuwal, Bilha, Ezem,

  4. Eltolad, Betul, Horma,

  5. Ziklag, Bet-Markabot, Hazar-Susa,

  6. Bet-Lebayot da Sharuhen, garuruwa goma sha uku ke nan da ƙauyukansu.

  7. Akwai kuma Ayin, Rimmon, Eter da Ashan, garuruwa huɗu ke nan da ƙauyukansu,

  8. da kuma dukan ƙauyukan da suke kewaye da garuruwan nan har zuwa Rama na Negeb (wato, Ba’alat-Beyer). Wannan shi ne gādon kabilar Simeyon bisa ga iyalansu.