Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Jews

231 ayoyi · 158 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina.

  2. Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.

  3. Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai.

  4. Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”

  5. Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji!

  6. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi ya shiga muku, za ku kuwa rayu.

  7. Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  8. Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi.

  9. Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.

  10. Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’ ”

  11. Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai.

  12. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’

  13. Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila.

  14. Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu.

  15. Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’ ”

  16. Ka riƙe sandunan da ka yi rubutun a gabansu

  17. ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan fitar da Isra’ilawa daga al’ummai inda suka tafi. Zan tattara su daga dukan kewaye in komo da su ƙasarsu.

  18. Zan mai da su al’umma ɗaya a cikin ƙasar, a kan duwatsun Isra’ila. Za a kasance da sarki guda a kan dukansu ba za su ƙara zama al’ummai biyu ko su rabu su zama masarautai biyu ba.

  19. Saboda halin kama-karyar da kika yi wa ɗan’uwanka Yaƙub, za ki sha kunya; za a hallaka ki har abada.

  20. A ranan nan kin tsaya kawai kina zuba ido yayinda baƙi suke washe dukiyar ɗan’uwanki, baƙi kuma suka shiga ta ƙofofinsa suka jefa ƙuri’a don a rarraba Urushalima, kin tsaya kina kallo kamar ɗaya daga cikin abokan gābansa.

  21. Bai kamata ki rena ɗan’uwanki a ranar masifarsa ba, ko ki yi farin ciki a kan mutanen Yahuda a ranar hallakarsu, ko ki yi fariya sosai a ranar wahalarsu.

  22. Bai kamata ki bi ta ƙofofin mutanena a ranar bala’insu ba, ko ki rena su a cikin masifarsu a ranar bala’insu, ko ki ƙwace dukiyarsu a ranar bala’insu ba.

  23. Bai kamata ki tsaya a mararraba don ki kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa ba, ko ki ba da waɗanda suka tsere ga hannun maƙiyansu a ranar wahalarsu ba.

  24. “Ranar Ubangiji ta yi kusa don dukan al’ummai. Kamar yadda kuka yi, haka za a yi muku; ayyukanku za su koma a kanku.

  25. Kamar yadda kuka sha a kan tuduna mai tsarki, haka dukan al’ummai za su yi ta sha, za su sha, su kuma sha su zama sai ka ce ba su taɓa kasancewa ba.