Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Jews: Idolatry
Ayoyi game da Idolatry
Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.
Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.
Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali;
suna zama a kaburbura su kwana suna yin asirtattun ayyuka; suna cin naman aladu, tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta;
suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.
“Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu
saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”