Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sheep: Watered every day

5 ayoyi · 63 fannoni

Ayoyi game da Watered every day

  1. Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”

  2. Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.

  3. Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila ’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.

  4. To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu.

  5. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.