Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Serpent

49 ayoyi · 16 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.

  2. Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,

  3. da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.

  4. Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela

  5. Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!

  6. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

  7. yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

  8. Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki; duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.

  9. In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin?

  10. Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso, ’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.

  11. Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,

  12. Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji.

  13. “Duba, zan aika macizai masu dafi a cikinku, kāsā, waɗanda ba su da maƙari, za su kuwa sassare ku,” in ji Ubangiji.

  14. Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, a can zan farauce su in cafko. Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, a can zan umarci maciji yă sare su.

  15. Za su lashi ƙura kamar maciji, kamar dabbobi masu rarrafe a ƙasa. Za su fito daga maɓuyarsu da rawan jiki, za su juya cikin tsoro ga Ubangiji Allahnmu su kuma ji tsoronku.

  16. Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji?

  17. “Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.

  18. Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”

  19. Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.

  20. Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba.

  21. Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne.

  22. Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.

  23. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.

  24. Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.