Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings

802 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”

  2. Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Lazarus, ka fito!”

  3. Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”

  4. Saboda haka Yahudawa da yawa da suka zo don su ziyarci Maryamu, suka kuma ga abin da Yesu ya yi, suka ba da gaskiya gare shi.

  5. Amma waɗansunsu suka je wurin Farisiyawa suka gaya musu abin da Yesu ya yi.

  6. Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.

  7. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.

  8. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.

  9. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

  10. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.

  11. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.

  12. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?

  13. To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?

  14. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,

  15. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma

  16. (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”

  17. A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”

  18. Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”

  19. Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.

  20. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!

  21. A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

  22. “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.

  23. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.

  24. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.

  25. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.