Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Satan

135 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”

  2. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’”

  3. Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.

  4. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama.

  5. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”

  6. Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

  7. Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.

  8. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;

  9. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”

  10. Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”

  11. Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

  12. Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.

  13. Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.

  14. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.”

  15. In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu.

  16. “Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.

  17. Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.

  18. Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”

  19. “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe kakamar alkama.

  20. Kullum ina tare da ku a filin haikali, amma ba ku kama ni ba. Amma wannan ne sa’a naku, lokacin da duhu yake mulki.”

  21. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”

  22. Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”

  23. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.

  24. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan.

  25. Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu.