Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Regeneration

256 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.

  2. “Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.

  3. Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.

  4. Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”

  5. Har yanzu ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya gauraye yistin duka.”

  6. Sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.

  7. Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”

  8. Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.

  9. A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.

  10. Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.

  11. Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”

  12. Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, “Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”

  13. Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

  14. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  15. Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.

  16. Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”

  17. Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.

  18. Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce,

  19. “Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.

  20. Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.”

  21. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

  22. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

  23. ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

  24. Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.

  25. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”