Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Purifications

66 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.

  2. “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.

  3. Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ”

  4. “ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,

  5. da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,

  6. duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.

  7. Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne.

  8. “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.

  9. Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.

  10. Bayan haka, dole firist yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka. Sa’an nan zai iya shiga cikin sansani, amma zai kasance da ƙazanta har yamma.

  11. Dole mutumin da ya ƙone ta yă wanke rigunarsa, yă kuma yi wanka, shi ma zai kasance da ƙazanta har yamma.

  12. “Mutumin da yake da tsarki, zai tara tokar karsanar, yă sa ta a wurin da yake da tsabta a bayan sansani. Jama’ar Isra’ilawa ne za su adana shi don amfani a ruwan tsabtaccewa; wannan domin tsarkakewa ne daga zunubi.

  13. Dole mutumin da ya tara tokar karsanar yă wanke rigunarsa, zai kuwa kasance da ƙazanta har yamma. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ta har abada ga Isra’ilawa, da kuma baƙin da suke zama a cikinsu.

  14. “Duk wanda ya taɓa gawa, zai kasance da ƙazanta har kwana bakwai.

  15. Dole yă tsarkake kansa da ruwa a rana ta uku, da kuma a rana ta bakwai; sa’an nan zai zama da tsarki. Amma in bai tsarkake kansa a rana ta uku da kuma a rana ta bakwai ba, ba zai kasance da tsarki ba.

  16. Duk wanda ya taɓa gawar wani, bai kuma tsarkake kansa ba, ya ƙazantar da tabanakul na Ubangiji ke nan. Dole a ware wannan mutum daga cikin Isra’ilawa. Gama ba a yayyafa ruwan tsabtaccewa a kansa ba; ya ƙazantu, ya kasance da ƙazanta ke nan.

  17. Sa’an nan wanda yake tsarkakakke, zai ɗauki hizzob yă tsoma a ruwa, yă yayyafa a tentin da dukan kayayyakinsa, da kuma a kan mutanen da suke wurin. Dole kuma yă yayyafa ruwan a kan duk wanda ya taɓa ƙashin mutu, ko kabari, ko kuma wanda aka kashe, ko wanda ya yi mutuwa ta Allah.

  18. Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta.

  19. Wannan za tă zama musu dawwammamiyar farilla. “Mutumin da ya yayyafa ruwa na tsarkakewa, shi ma dole yă wanke rigarsa. Duk wanda kuma ya taɓa ruwan tsarkakewa, zai kasance da ƙazanta har yamma.

  20. Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.

  21. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,

  22. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

  23. Na wanke hannuwana cikin rashin laifi, ina yawo a bagadenka Ya Ubangiji,

  24. Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  25. “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”