Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Punishments: Scourging
Ayoyi game da Scourging
in mai laifin ya cancanci bulala, alƙali zai sa yă kwanta a yi masa bulala a gabansa da yawan bulalan da ya dace da laifin,
amma kada yă yi masa bulala fiye da arba’in. In ya yi masa fiye da haka, za a ƙasƙantar da ɗan’uwanku, zai kuma zama rainanne a idonku.
Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”
Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.