Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Obedience

136 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne.

  2. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.

  3. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”

  4. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.

  5. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.

  6. “In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.

  7. Yesu ya amsa ya ce, “Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.

  8. amma dole duniya ta koya cewa ina ƙaunar Uba, ina kuma yin yadda Ubana ya umarce ni. “Ku zo, mu bar nan.

  9. In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.

  10. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.

  11. Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.

  12. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.

  13. Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!

  14. Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku.

  15. Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  16. Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,

  17. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  18. Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.

  19. Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

  20. Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci,

  21. waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.

  22. Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.

  23. Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa.

  24. Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa.

  25. Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.