Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Missions: General references

48 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.”

  2. Saboda haka ɗaya daga cikin firistocin da aka kawo bauta daga Samariya ya dawo ya zauna a Betel, ya koya musu yadda za su yi sujada ga Ubangiji.

  3. Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.

  4. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

  5. Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka.

  6. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

  7. Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.

  8. Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo ’ya’yana maza daga nesa ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,

  9. kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”

  10. Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.

  11. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

  12. Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.

  13. A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”

  14. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.

  15. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.

  16. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.

  17. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.

  18. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.”

  19. Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.

  20. Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikinsunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,

  21. Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.

  22. Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.

  23. Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.

  24. Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

  25. Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.