Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Millennium

41 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.

  2. Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada a abin da na halitta, gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna mutanenta kuwa abin farin ciki.

  3. Zan yi farin ciki a kan Urushalima in kuma yi murna saboda mutanena; a can ba za a ƙara jin karar makoki da na kuka ba.

  4. “A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne.

  5. Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu; za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu.

  6. Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba, ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba. Gama kamar yadda kwanakin itace suke, haka kwanakin mutanena za su kasance; zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin ayyukan hannuwansu.

  7. Ba za su yi wahala a banza ba ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a; gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka, su da zuriyarsu tare da su.

  8. Kafin su yi kira zan amsa; yayinda suke cikin magana zan ji.

  9. Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji.

  10. A wannan rana ba za ku sha kunya saboda laifofin da kuka yi mini, gama zan ɗauke wa wannan birni waɗanda suke farin ciki cikin girmankansu. Ba kuma za ka ƙara yin kallon reni a tuduna mai tsarki ba.

  11. Amma zan zauna a cikinki masu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai, waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji.

  12. Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba, ba za su faɗa ƙarya ba, ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba. Za su ci su kuma kwanta kuma babu wanda zai ba su tsoro.”

  13. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.

  14. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.

  15. Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul.

  16. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba.

  17. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.

  18. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.

  19. A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade.

  20. Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.

  21. Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba.

  22. Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”

  23. Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”

  24. Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

  25. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.