Skip to content

Gog

8 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Gog

  1. “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa

  2. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.

  3. “Saboda haka ɗan mutum, ka yi annabci ka ce wa Gog, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar, sa’ad da mutanena Isra’ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba?

  4. Za ka ci gaba a kan mutanena Isra’ila kamar yadda girgijen yakan rufe ƙasa. A kwanaki masu zuwa, ya Gog, zan kawo ka, ka yi yaƙi da ƙasata, domin al’ummai su san ni sa’ad da na nuna kaina mai tsarki ta wurinka a gabansu.

  5. Ga abin da zai faru a ranar. Sa’ad da Gog ya fāɗa wa ƙasar Isra’ila, fushina mai zafi zai ƙuna, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  6. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.

  7. “ ‘A ranar zan yi wa Gog makabarta a cikin Isra’ila, a kwarin waɗanda suke tafiya wajen gabashin Teku. Za tă tare hanyar matafiya, domin za a binne Gog da dukan mutanensa a can. Ta haka za a kira wurin Kwarin Haman Gog.

  8. zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.