Tsallake zuwa abun ciki

Tubal

5 verses

40.9000, 37.7900 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Tubal

  1. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.

  2. “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.

  3. “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa

  4. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.

  5. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.