Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tubal

8 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.

  2. ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.

  3. “Zan kafa alama a cikinsu, zan kuma aika waɗansu da suka tsira zuwa al’ummai, zuwa Tarshish, zuwa Libiya da Lidiya (sanannun ’yan aika), zuwa Tubal da kuma Girka, da kuma zuwa manisantan tsibirai da ba su taɓa jin labarin sunana ba ko su ga ɗaukakata. Za su yi shelar ɗaukakata a cikin al’ummai.

  4. “ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.

  5. “Meshek da Tubal suna can, tare da dukan jama’arsu kewaye da kaburburansu. Dukansu marasa kaciya ne, da aka kashe da takobi domin sun haddasa tsoronsu a ƙasar masu rai.

  6. “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog, na ƙasar Magog, babban sarkin Meshek da Tubal; ka yi annabci a kansa

  7. ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.

  8. “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan Gog ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da kai, ya Gog, babban sarkin Meshek da Tubal.