Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Liberality

149 ayoyi · 55 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku.

  2. Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

  3. Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai

  4. a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari,

  5. kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”

  6. Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.

  7. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.

  8. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

  9. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”

  10. To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.

  11. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

  12. Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.

  13. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.

  14. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.

  15. Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;

  16. gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.

  17. Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.

  18. Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.

  19. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

  20. Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?

  21. A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,

  22. sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?

  23. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?

  24. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.