- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Liberality
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
Waƙar haurawa. Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
“Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,
ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,
sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.
Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
Ka jefa burodinka a bisa ruwaye, gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas, gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
‘Daga wannan rana zuwa gaba, wato, rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, ku lura da ranar da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji. Ku lura da kyau.
Akwai sauran irin da ya rage a rumbu? Har yanzu, kuringar inabi da itacen ɓaure, rumman da itacen zaitun ba su ba da ’ya’ya ba tukuna. “ ‘Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’ ”
Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.
“Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.
Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi,
don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”
Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.