Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Lasciviousness

68 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mijina ba ya gida; ya yi tafiya mai nisa.

  2. Ya ɗauki jakarsa cike da kuɗi ba zai kuwa dawo gida ba sai tsakiyar wata.”

  3. Da kalmomin rarrashi ta sa ya kauce; ta ɗauki hankalinsa da sulɓin maganarta.

  4. Nan take, ya bi ta kamar saniyar da za a kai mayanka, kamar wawa zuwa wurin da za a ba shi horo

  5. sai da kibiya ta soki hantarsa, kamar tsuntsun da ya ruga cikin tarko, ba tare da sani zai zama sanadin ransa ba.

  6. Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni; ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

  7. Kada ku bar zuciyarku ta juya zuwa hanyoyinta ko ku kauce zuwa hanyoyinta.

  8. Ta zama sanadin fāɗuwar yawanci; kisan da ta yi ba ta ƙidayuwa.

  9. Gidanta babbar hanya ce zuwa kabari mai yin jagora zuwa ɗakunan lahira.

  10. Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.

  11. Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,

  12. tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.

  13. “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.

  14. “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”

  15. Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.

  16. “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,

  17. yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

  18. “Ga yadda mazinaciya take yi. Takan ci ta share bakinta ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’

  19. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,

  20. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.

  21. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”

  22. Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye,

  23. suka kuma yi musayar ɗaukakar Allah marar mutuwa da siffofin da aka ƙera su yi kama da mutum mai mutuwa da tsuntsaye da dabbobi da kuma halittu masu ja da ciki.

  24. Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya.

  25. Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.