Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Gethsemane

43 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.”

  2. Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.

  3. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

  4. Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

  5. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?

  6. Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

  7. Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

  8. Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.

  9. Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.

  10. Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi.

  11. Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”

  12. Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.

  13. To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.”

  14. Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.

  15. Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.” Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi.

  16. Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”

  17. Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.

  18. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”

  19. Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a.

  20. Ya ce, “Ya Abba,Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”

  21. Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya?

  22. Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

  23. Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi.

  24. Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.

  25. Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.