Skip to content

Judas

23 ayoyi · 1 ɗan gida

An kuma san shi da: Judas Iscariot, Iscariot

Ayoyin da suka ambaci Judas

  1. Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

  2. Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci

  3. Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”

  4. Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su.

  5. Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.

  6. da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

  7. Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.

  8. Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.

  9. Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

  10. Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.

  11. Yana cikin magana sai ga taro sun zo. Mutumin nan da ake kira Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun, shi ya bi da su. Sai ya matso kusa da Yesu don yă yi masa sumba.

  12. Amma Yesu ya tambaye shi ya ce, “Yahuda, ashe, da sumba za ka bashe Ɗan Mutum?”

  13. (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)

  14. Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce,

  15. Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu.

  16. Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.

  17. Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu.

  18. Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, “Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?”

  19. To, Yahuda, wanda ya bashe shi, ya san wurin, domin Yesu ya sha zuwa wurin da almajiransa.

  20. Saboda haka Yahuda ya zo cikin lambun, yana jagoranta ƙungiyar sojoji da waɗansu ma’aikata daga wurin manyan firistoci da Farisiyawa. Suna riƙe da toci, fitilu da kuma makamai.

  21. Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, “Ni ne shi.” (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.)

  22. ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu

  23. ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.”