Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Covenants

42 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su.

  2. Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.

  3. Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.

  4. Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu.

  5. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.

  6. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”

  7. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

  8. “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”

  9. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”

  10. Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir.

  11. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”

  12. A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata.

  13. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.

  14. waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.

  15. Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya.

  16. Ko da yake suna da shugabanni a Zowan kuma jakadunsu sun iso Hanes,

  17. kowa zai sha kunya saboda mutanen da ba su da amfani gare su, waɗanda ba sa taimako ko amfani, sai dai jawo kunya da da-na-sani.”